Ana samun ci-gaba a yakin da cutar AIDS a wasu kasashe na Afirka | Labarai | DW | 14.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana samun ci-gaba a yakin da cutar AIDS a wasu kasashe na Afirka

Bankin duniya ya ce ana samun ci-gaba a yakin da ake yi da cutar AIDS ko Sida a nahiyar Afirka. A cikin wani rahoto da ya bayar a Kigali babban birnin kasar Rwanda, bankin ya ce akwai alamun cewa a wasu kasashen nahiyar ta Afirka, kwayoyin cutar ba sa yaduwa da sauri kamar a lokutan baya. To amma haka ba ya nufin an daina kamuwa da cutar wadda kawo yanzu ta yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin miliyan biyu sannan wasu miliyan 25 ke dauke da kwayoyin ta ba. bankin ya ce ana samun nasarar yaki da cutar ta AIDS a kasashe kamar Uganda, Kenya da Zimbabwe sai kuma a wasu manyan birane na kasashen Habasha, Rwanda da kuma Zambia. To amma ba wani canji na a zo a gani a kasahen yankin kudancin Afirka. A cikin rahoton bankin duniya ya ce tun daga shekara ta 2000 ya kashe kudi Euro miliyan 600 don yakar AIDS.