1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana nuna shakku kan zaben Kwango

December 11, 2018

Masu kallon lamura irin na siyasa na dora alamun tambayoyi kan samun natsuwa a zaben kasar Kwango da ke tafe.

https://p.dw.com/p/39pib
Congolese presidential contender Etienne Tshisekedi
Hoto: DW/S. Mwanamilongo

Yayin da babban zaben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ke kara karatowa, masu kallon lamura na hasashen iya samun matsaloli a zaben, duk da cewar harkokin yakin zabe na tafiya ba tare da gagarumar matsala ba.

A ranar 23 ga wannan watan na Disamba ne dai ake sa ran gudanar da zaben, wanda kungiyar Tarayyar Turai ta sake sabonta takunkuminta a kan dan takaran da Shugaba Joseph Kabila ya tsayar, Emmanuel Ramazani Shadary.

Shugaban na Kwango Joseph Kabila ya kuma bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara bayan karewar wa'adin wanda zai karbi ragamar kasar a zaben da ke tafe.

Mr. Kabilan dan shekaru 47, wanda ya gaji mulki a hannun mahaifinsa a shekara ta 2001 ya yi alkawarin samar da zabe karbabbe duk da shakkun da kasashen duniya ke nunawa.