Ana neman sulhunta rikicin majalisar Nijar | Siyasa | DW | 09.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana neman sulhunta rikicin majalisar Nijar

An girka wani kwamiti da ya hada bangarorin da ke takun saka a majalisar dokokin Nijar domin kashe wutar rikicin da ya kunno kai tsakanin kakakin da bangaren gwamnati.

Kwanaki 20 aka shafe ba tare da majalisar dokokin Nijar ta gudanar da aikinta yadda ya kamata ba. Dalili kuwa shi ne, jam'iyyun da ke kawance da gwamnati suna takun saka tsakaninsu dangane da rabon mukamai a majalisar. A hakikanin gaskiya dai, bangaren PNDS Tarayya ta shugana Issoufou na neman tsige kakakin majalisar Hama Amadou na Modem Lumana. Sai dai shi ya ce ba za ta sabu ba idan aka yi la'akari da yarjejeniyar da ke tsakaninsu da kuma dokokin majalisar.

Sai dai kuma bangarorin biyu na PNDS da kuma Modem Lumana sun zauna a karkashin wani kwamiti a birnin Yamai domin yin nazari tare da magance rashin fahimtar da ke tsakaninsu. Rahotonnin da ke zuwa mana daga Nijar sun nunar da cewa wasu 'yan majalisa na bangaren adawa da suka bijire wa jam'iyyunsu domin mara wa jam'iyyar PNDS baya ne bangaren da ke mulki ke neman saka musu da mukamai a majalisar ta dokoki.

Mawallafi: Mahaman Kanta
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin