Ana neman riga-kafin cutar Ebola | Zamantakewa | DW | 04.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ana neman riga-kafin cutar Ebola

Sama da mutane dubu 10 suka mutu sakamakon cutar Ebola a yankin yammacin Afirka. An samu raguwar masu kamuwa da cutar, amma har yanzu ba a shawo kanta ba

Tuni dai masana kimiyya a fadin duniya suka dukufa wajen nemo allurar riga-kafin cutar ta Ebola. Kasar Gabon na daga cikin wuraren da masu binciken kimiyya ke aikin samun allurar riga-kafin.

Tun a karshen shekarar bara shi dai matashin ya zama zakaran gwajin dafi na allurar riga-kafin cutar Ebola, tun sannan ne kuma zuwa asibitin don duban jinisa ya zama masa jiki.

Jose Fernandez shi ne likita wanda kuma ke jagorantar binciken kimiyya. Ya katse karatun neman digirin digirgir a Jamus don gudanar da binciken.

A dakin binciken kimiyya da ke kauyen Lambaréné a kasar Gabon ake bincken allurar riga-kafin mai suna VSV-ZEBOV da wani bangarensa ke kunshe da kwayar cutar Ebola. Fatan masu binciken shi ne garkuwar jikin wanda aka yi wa allurar ta yaki kwayoyin cutar. Sannan a mataki na gaba a yi gwajin ingancin allurar riga-kafin a kasashen da ke fama da Ebola.

A wurare daban-daban a Amirka da Turai da kuma Afirka ake gudanar da bincike karkashin kulawar hukumar lafiya ta duniya WHO, inji Bertram Lell mai kula da aikin a kauyen Lambaréné da ke kasar Gabon inda masu binciken kimiyya ke aiki kafada da kafada da kwararru na cibiyar binciken cututtukan yankuna massu zafi da ke garin Tübingen na Jamus.

Yanzu dai kauyen na Lambaréné da ke cikin kurmin dajin kasar ta Gabon ya zama cibiyar binciken cutar Ebola. Wannan dai na da dalilai na tarihi domin cibiyar binciken na kusa da asibitin da Albert Schweitzer da ya taba samun kyautar zaman lafiya ta Nobel ya gina. Shi dai Albert Schweitzer likita ne kuma dan asalin kasashen Jamus da Faransa ne kuma ya rasu a ranar 4 ga watan Satumabn 1965 a kauyen na Lambaréné. Masu binciken na fata idan komai ya tafi yadda aka tsara a cikin wasu makonni za a fara amfani da allurar riga-kafin kai tsaye a yankuna masu fama da Ebola.