1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kara samun ci gaban tashe-tashen hankulla a yankin Darfur

YAHAYA AHMEDOctober 11, 2005

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwarta ga yiwuwar barkewar wata annoba ta kisan kiyashi a yankin Darfur. Babban jami'in majalisar, mai kula da batun yin riga kafin kisan kare dangi, Juan Mendez ne ya bayyana haka a wani taron maneman labarai a birnin New York.

https://p.dw.com/p/BvYv
Sansanin `yan gudun hijira a yankin Darfur
Sansanin `yan gudun hijira a yankin DarfurHoto: dpa

Da yake bayani kan yadda al’amura ke ci gaba da tabarbarewa a yankin Darfur, wakilin Majalisar Dinkin Duniyar, Juan Mendez, ya yi matashiya da irin ababan da suka wakana a yankin a shekara ta 2003, inda mayakan kungiyar larabawan nan ta Janjaweed, tare da daurin gindin sojojin gwamnati, suka yi ta afka wa kauyuka, suna halaka mazauna da kuma ragargaza matsugunansu. Kusan mutane miliyan 2 ne suka kasance makaurata, sakamakon wannan tashin hankalin.

To sai ga shi a yanzu kuma, wannan matsalar na barazanar sake kunno kai, inji babban jami’in na Majalisar Dinkin Duniya, Mendez. Ya kara da cewa:-

„`Yan harin, suna zuwa ne kan rakuma da kuma motocin sojin gwamnatin Sudan.“

A da can dai, Amirka ta fara zargin gwamnatin birnin Khartoum da ga daure wa masu kisan kiyashi a yankin na Darfur gindi. To yanzu ne ma wannan danyen aikin zai wakana sosai, inji jami’in, tun da a nasa ganin gwamnatin birnin Khartoum ba ta daukan ko wane mataki na cika ka’idojin Majalisar Dinkin Duniyar:-

„Gwamnatin ta birnin Khartoum ba ta ba da hadin kai ga kotun kasa da kasa, kamar yadda kwamitin sulhu ya bukace ta ta yi. Kazalika kuma, watanni da dama bayan cikar wa’adin da kwamitin koli na majalisar ya ajiye mata, gwamnatin ba ta bayyana wani mataki na kwance wa mayakan janjaweed din damara ba.“

Gamayyar kasa da kasa dai, ta janye jiki ne kawai tana sa wa dakarun kungiyar Tarayyar Afirka ido, da fatar cewa za su iya magance matsalar. Amma har ila yau, an ata jiran taimakon kudin da gamayyar ta yi alkawarin za ta bayar. Mendez ya bayyana takaicinsa ga halin da ake cikin ne da cewa:-

„Mun tura dakarun kungiyar AU zuwa wani aikin da ba za su iya kammalawasu kadai ba. Yanzu ne kuwa ya kamata mu taimaka musu.“

Shi dai babban jami’i Mendez na mai ra’ayin cewa, zaman ba ruwanmu da rashin angaza wa gwamnatin Sudan ta dau matakan hana ci gaban tabarbarewar al’amura a yankin na Darfur da gamayyar kasa da kasa ke yi, zai kasance wata barazana ga tabbatad da zaman lafiya a yankin:-

„Mun ceto mutane da yawa daga halaka. A lokaci daya kuma mun tabbatad da kwanciyar hankali a yankin. Amma yanzu ana huskantar barazanar tabarbarewar al’amura.“

Mendez dai ya fi bayyana takaicinsa ne ga babakeren da jakadan Amirka a Majalisar Dinkin Duniyar, John Bolton ya yi masa, na hawan kujerar na ki, don hana shi bayyana gaban kwamitin sulhun ya gabatad da rahotonsa.

A nasa bangaren jakadan Amirkan, John Bolton, ya bayyana cewa, ya dau wannan mataki ne, saboda kwamitin sulhun ya gaji da sauraron rahotanni daban-daban da ake gabatar masa kan yankin na Darfur. Ya kaara da cewa, yanzu abin da ya kamata a yi ne, a fara daukan sahihan matakai kan wannan matsalar. Sai dai, a daura da wasu lokuta na baya, har ila yau Amirka ba ta fito fili ta gabatad da ra’ayinta kan irin matakin da ya kamata a yanke ba.