Ana juyayin rasuwar ministan cikin gidan kasar Cuba | Labarai | DW | 08.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana juyayin rasuwar ministan cikin gidan kasar Cuba

Majalisar ministocin Cuba ta sanar da rasuwar ministan cikin gidan kasar Carlos Fernandez Gondin wanda ya rasu a ranar Asabar a birnin Havana fadar gwamnatin kasar.

Ministan marigayi mai shekaru 78 da haihuwa, ya rasu ne sakamakon rikicewar jikinsa dangane da wata rishin lafiya da ta dade tana damunsa. Marigayin wanda kuma babban Janar ne na sojan kasar ta Cuba, kuma daya daga cikin shika-shikan juyin juya halin kasar, na rike da wannan mukami ne na ministan cikin gida tun daga shekara ta 2015 bayan da ya canji wani kusa na juyin juya halin kasar Abelardo Colome Ibarra, wanda ya nemi da shugaban kasar ya yi ma sa ritaya.

Shi dai marigayin Carlos Fernandez Gondin, an haifeshi ne a birnin Santiago da ke gabashin kasar ta Cuba, kuma ya kasance daya daga cikin jagororin sojojin Cuba a kasar Angola a shekarun 1980 da 1990.