Ana gudanar da zabe a kasar Kwango | Labarai | DW | 30.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana gudanar da zabe a kasar Kwango

Rahotanni daga Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Demokradiyar Kwango sun bayyaana yadda al'ummar kasar suka fara kada kuri'un su a cikin fargaba bullar sabon rikici a kasar

Mafiya yawan masu ka'da kuri'un na da burin zaben wanda zai gaji shugaba Joseph Kabila wanda ya kamata ace ya jima da sauka da mulkin kasar. Hkumar zaben kasar  ta umarci jami'anta su bude cibiyoyin zaben tun da misalin karfe hudu na asuba a Lubumbashi da ke yankin gabashin kasar bayan sanar da karfe hudu na yamma a matsayin lokacin na kammala zaben a dukkanin mazabun kasar.

Aa nasu bangaren masu takara daga jam'iyyun adawa sun yi watsi da bukatar rattaba hannu kan yarjejeniyar gudanar da zaben lafiya bayan sun zargi hukumar da son rai. Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya da kasar Amirka da kuma kasashen Turai suka bukaci hukumar zaben kasar ta yi duk mai yiwuwa don ganin an gudanar da sahihin zabe, Su ma shugabannin kasashen Angola da Botswana da Namibiya da Zambiya da sauran kasashe makwabta sun bukaci a gudanar da wannan zabe lafiya.