Ana gudanar da zaɓe a nahiyar Turai | NRS-Import | DW | 25.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Ana gudanar da zaɓe a nahiyar Turai

Miliyoyin mutane da suka cancanci yin zaɓe na ci gaba da kaɗa ƙuri'a a ƙasashen Turai daban-daban domin zaɓen wakilai 751 na majalisar dokokin Turai .

Al'umma a cikin ƙasashe 21 bisa 28 da suka yi saura na nahiyar Turai na jefa ƙuri'a a zaɓen majalisar dokokin Turai. Mutane kamar miliyam dubu 388 waɗanda suka cancanci yin zaɓen, za su kaɗa ƙuri'a domin zaɓen wakilan 'yan majalisu 751 na nahiyar, a cikin ƙasashen Girka da Jamus da Faransa da dai sauransu a wani wa'adin mulki na shekaru biyar.

Sannan kuma za a zaɓi shugaban ƙungiyar da kuma wanda zai jagoranci majalisar zartarwa na Kungiyar Gamayyar Turai.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe