1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana guidanar da zaɓen 'yan majalisun dokoki a Turkiya

Abdourahamane HassaneJune 7, 2015

Jam'iyyar da ke yin mulki ta AKP na neman rinjaye a zaɓen domin canza kudin tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/1Fcrr
Türkei Wahlen (Symbolbild)
Hoto: picture-alliance/dpa/U. Deck

Al'umma Turkiya na kaɗa ƙuri'a a zaben yan majalisuin dokokin wanda shi ne irinsa mafi kankan da ake ganin za a yi a cikin shekaru goma a ƙasar jam'iyyar da ke yin mulki ta AKP na neman samun rinjaye a majalisar domin canza kudin tsarin mulki.

Don samar da cikakken iko ga shugaban ƙasa wato a maimakon tsarin mulki mai ruwa biyu wanda firaministan ne ke da cikkaken iko.Sai dai jam'iyyar da ke yin mulki na fuskantar ƙalubale na jam'iyyar Ƙurdawa ta HDP wacce idan ta samu kishi 10 cikin ɗari na ƙuri'un za ta iya dagulawa jam'iyyar ta AKP lisafi.