Ana gudanar da bincike a Amirka | Labarai | DW | 17.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana gudanar da bincike a Amirka

Bayan harin da wani tsohon jaim'in sojin ruwa na ƙasar ya kai a kan ginin cibiyar sojojin ruwan a Washington wanda a ciki ya harbe mutane 12, kafin a kashe shi.

Jami'an tsaron Amirka sun ce sun fara gudanar da bincike da ma dai tattara sakamako dangane da dalilan harin da wani ɗan bindigar ya kai wa wani ginin sojin ruwan ƙasar a jiya Litinin wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutane sha uku ciki har da ɗan bindigar, baya ga wasu da dama da suka jikkata.

Tuni dai jami'an tsaro na FBI suka bayyana sunan Aaron Alexis wanda a baya jami'i ne na sojin ruwan ƙasar a matsayin wanda ke da hannu wajen hari har ma abokansa sun fara ba da ba'asi dangane da hallayyarsa inda wasu ke cewar kamili ne, sai dai sun ce akwai wata jiƙaƙƙiya tsakaninsa da rundunar sojin ruwan ƙasar.

Gwamnatin AmIrka ta nuna damuwarta dangane da wannan hari inda shugaba Barack Obama ya ba da ummarnin sassauto da tutocin ƙasar ƙasa-ƙasa har ranar Jumma'a don yin alhinin waɗanda suka rasu a ƙoƙarinsu na kare al'ummar ƙasar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohamadou Awal Balarabe