SiyasaRuwanda
Ana gudanar da babban zaben kasa a Ruwanda
July 15, 2024Talla
Miliyoyin 'yan kasar ta Ruwanda ne dai za su kada kuri'a a wannan Litinin, a zaben da ake ganin Shugaba Paul Kagame ne zai iya lashewa inda zai yi mulki wasu shekaru biyar.
Tun a shekara ta 2000 ne dai Paul Kagame ke mulki a Ruwandar, bayan kawo karshen kisan kiyashin kasar da aka yi a shekara ta 1994.
'Yan takara biyu ne ke fafata da Shugaba Kagame, bayan haramta wa wasu fitattun masu sukar lamirin gwmanatinsa da aka yi.
'Yan takarar dai su ne Frank Habineza, jagoran jam'iyyar Democratic Green Party da kuma dan takarar Indifenda Philippe Mpayimana.
Wannan ne karo na hudu da Paul Kagame ke takara a Ruwanda.