1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fuskantar matsalar walwala a intanet a Afirka

Ramatu Garba Baba MAB
November 5, 2019

A wani rahoto da Kungiya ta Freedom on the Net ta fitar a wannan shekara ta 2019 ta bayyana damuwa a game da yadda 'yancin fadin albarkacin baki ta shafukan sada zumunta ke fuskantar koma-baya a wasu kasashen Afrika.

https://p.dw.com/p/3SVWh
Symbolbild Afrika Medienentwicklung Digitale Medien
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo


Rahoton Kungiyar ya bayyana manyan kalubalen da masu mu'amala da kafafen sada zumunta ke fuskanta bayan matakan gwamnatoci da ke katse ko yin kutse a wasu lokuta don  tatsar bayanan jama'a, ana kuma daukar mataki don taka wa duk mai adawa birki. Rahoton Kungiyar ya ci gaba da cewa, hakan mataki ne da ya tauye 'yanci na fadin albarkacin baki da jama'a ke yi ta kafafen sadarwar zamani.


Isabel Linzer na daga cikin masu kare 'yancin jama'a, ta ce batu ne da ke kara kamari inda ta ce ''Matakin ya shafi fakewa da sunan binciken sirri da manyan jami'ai suke yi wa shafukan sada zumunta na jama'a, matsala ce babba a kasashen yankin Sahara kamar Kenya da Afirka ta Kudu da Angola da Najeriya da kuma Yuganda''

Symbolbild: Computertechnologie und digitales Afrika
Matasa na nakaltar inji mai kwakwalwa a kasashen AfirkaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

A kasa kamar Zimbabuwe kuwa, gwamnati na sanya dokar da za ta bai wa jami'an gwamnati damar bibiya da ma saka ido kan rubuce-rubucen jama'a ta yi, muradunsu shi ne su gani sun hana duk wata adawa da gwamnati, baya ga haka akwai doka mai karfi da gwamnati ke da ita na kwace kwamfutocin jama'a su kuma shiga runbunan bayanai inji Munya Bloggo fittacen marubuci na shafukan sada zumunta. Ya ce "Mataki ne na hana jama'a 'yanci fadin albarkacin bakinsu, na jefa su cikin fargaba don kuwa kowa na taka tsantsan gudun fadawa hannu hukuma.''


A kasar Sudan kuwa, duk da an yaba da rawar da kafafen sadarwar suka taka a yayin rikicin kasar da ya kai ga hambarrar da gwamnatin Omar al-Bashir, wakilin DW  a Sudan Sanosi Osman, ya ce gara a hanzarta taka wa kasashe masu wannan dabi'a birki.

BG Frauen im Sudan
Intanet ya taimaka wajen yada wakar Alaa Saleh a boren juya hali a SudanHoto: Getty Images/AFP

Ya ce " Ba don kafaffen sadarwa kamar su Facebook da Instagram da kuma Whatsapp da Twitter da suka taka muhimmiyar rawa a rikicin Sudan, ai da wuya a ma san halin da kasar ta fada, saboda haka idan za a ci gaba da katse layukan sadarwa da yi wa shafuka kutse, to nan gaba jama'a za su nemi mafita, ta hanyar bijirewa gwamnati, za su fantsama kenan kan tituna''


Kungiyar ta Freedom on the Net Report  na ganin gwamnati na da damar gindaya sharudda kan batutuwan da suka shafi zabuka amma kuma ta bayar da 'yancin fadin albarkacin baki, aiki ne da ta ce ya rataya a wuyan kungiyoyin farar hula, su matsa kaimi har sai an cimma kawar da amfani da matakin karfi a kan masu amfani da shafukan sadarwar na yanar gizo..