Ana farautar wasu ma′aikata 100 a Turkiya | Labarai | DW | 02.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana farautar wasu ma'aikata 100 a Turkiya

Ana zargin wasu jami'an asibitin sojoji da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan.

Gwamnatin kasar Turkiya ta sake bada umarnin kame wasu ma'aikata 100 ciki har da wasu manyan likitoci a asibitin sojoji da ke birnin Ankara. Jami'an gwamnatin kasar sun bayyana wannan yunkuri a matsayin bude sabon babin bincike a kan yunkurin kifar da gwamnatin Recep Tayyib Erdogan da bai cimma nasara ba a watan da ya gabata.

Ana dai zargin wasu ma'aikatan asibitin da bai wa 'yan kungiyar Fethulla Gulen bayanan sirri, wannan ya sa gwamnatin ke daura alhakkin yunkurin juyin mulkin a kan kungiyar ta Fethulla Gulen.

Gwamnatin Erdoan ta kori dubban ma'aikata a matakai daban-daban ciki har da na soje tun bayan yunkurin juyin mulki.