Ana faragabar sake bayyanar Ebola a Saliyo | Labarai | DW | 15.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana faragabar sake bayyanar Ebola a Saliyo

Kasar Saliyo ta ba da sanarwar a jiya Alhamis soma gudanar da bincike kan mutuwar wani dan kasar tata da ya rasu a wani gidan assibiti na kasar da kuma binciken farko ya nunar da cewar cutar Ebola ce ta kashe shi .

Kasar Saliyo ta sanar a jiya Alhamis da soma gudanar da bincike kan mutuwar wani mutun dan kasar tata da ya rasu a wani gidan assibiti na garin Magburaka na cikin karamar hukumar Tonkolili a Arewacin kasar da kuma ake kyatata zaton cutar Ebola ce ta kashe shi .

Wani jami'in ofishin ministan kiwon lafiya na kasar ta Saliyo ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa wani binciken farko da suka gudanar a kan gawar mutuman a jiya Alhamis ya nunar da cewa Ebolar ce ta kashe shi. Amma kuma za su kara gudanar da karin wani binciken wanda ake sa ran bayyana sakamakonsa a wannan Jumma'a.Wannan warwarewar asalati ta zo ne kwanaki kalilan bayan da Hukumar lafiya ta Duniya WHO ko OMS ta bayyana kawo karshen cutar ta Ebola a kasar Laberiya dama illahirin kasashen yankin da suka yi fama da cutar a tsawon shekaru biyu.