1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fara taron shekara-shekara

September 24, 2013

A wannan Talata ake fara babban taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara.

https://p.dw.com/p/19moH
Hoto: Getty Images

Shugabannin kasashen duniya na hallara wannan Talata domin fara zaman babban taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara karo na 68, da ke gudana a birnin New York na kasar Amirka.

Maganar nukiliyar Iran da rikicin kasar Sirina na cikin abubuwan da za su mamaye tattaunawar. Sabon shugaban kasar Iran Hasan Rouhani na cikin wadanda za su gudanar da jawabai.

Fadar mulkin kasar Amirka ta White House, ta ce ba ta fid da ran yiwuwar wata saduwa tsakanin Shugaban Amirka Barack Obama da sabon shugaban na Iran Hasan Rouhani a gefen babban taron mashawartar Majalisar Dinkin Duniya ba. Sai dai sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry, zai halarci wani taro da wakilan manyan daulolin duniya za su da ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif a wannan mako a kan shirin nukiliyar Iran.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu