Ana fafatawa tsakanin mayaka a birnin Bambari | Labarai | DW | 02.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana fafatawa tsakanin mayaka a birnin Bambari

Rahotanni daga Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya na cewa, a ana ci gaba da fafatawa tsakanin mayaka na Anti-Balaka da Fulani a garin Bambari.

A wani sabon adadi na baya-bayannan da ofishin jandarmomin wannan kasa ya bayar, yace a kalla mutane 25 suka rasu wasu kuma da dama suka samu raunuka. Rahotannin na cewa ana ci gaba da wannan fada tsakanin mayakan dake kiran kansu 'yan Anti-Balaka, da Musulmi 'yan kabilar Fulani a cewar wannan majiya. Mutane da dama dai daga cikin mazamna wannan birni sun samu mafaka a wani Cocin Katolika kafin wannan rikici ya lafa.

A jiya Laraba ma dai dakarun Faransa sun sanar da kashe a kalla mutane bakoye daga cikin mayakanwannan yanki inda suka ce sun buda wuta ne ga dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya na Minusca dake ayukan tsaro a wannan kasa a cewar kakakin rundunar sojojin kasar ta Faransa, inda daga bisani mayakan suka kai hari tare da sace kayayakin kungiyoyi masu zaman kasu dake wannan birni, har ma dana kungiyar agaji ta red Cross.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu