Ana dab da soma babban taron AU a Nijar | Siyasa | DW | 04.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana dab da soma babban taron AU a Nijar

Yanzu haka dai birinin Yamai na Jamhuriyar Nijar ya dauki sabon harami, inda wakilai na gwamnatoci da shugabannin ke ci gaba da zuwa domin yin taruka share fage gabannin taron na AU.

Shugaba hukumar gudanarwa na kungiyar ta AU Moussa Faki Mahamat wanda ya kaddamar da taron a birnin Yammai ya ce taron zai kasance tarihi game da yadda za a kaddamar da shirin kasuwanci marasa shinge a tsakanin kasashen Afirka a wannan taro. An shirya ranakun Asabar da Lahadi za su kasance ranakun da taron zai kasance a kololuwarsa tare da halarta shugabanni daga sassa dabam-dabam na Afirka. A share daya kuma hukumomin Nijar sun kara karfafa tsaro sakamakon barzanar da ake fuskanta daga 'yan ta'adda na kai hare-hare.

Sauti da bidiyo akan labarin