Ana cigaba da zaman zulumi a Mogadishu | Labarai | DW | 07.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana cigaba da zaman zulumi a Mogadishu

Mayakan sa kai masu biyayya ga haɗaɗɗiyar ƙawancen madugan yaki dake samun goyon bayan Amurka sun ja daga a muhimman wurare a arewacin Mogadishu babban birnin ƙasar Somalia. Garin Jowhar mai tazarar kilomita 75 arewa maso yammacin Mogadishu na ƙarƙashin kulawa ne ta haɗaɗɗiyar ƙungiyar madugan yaƙi. Rahotanni sun baiyana cewa mayakan ƙungiyoyin madugan yaƙin na shirin maida martani a kan mayaƙan Islama waɗanda suka kore su daga birnin Mogadishu a ranar litinin data wuce. A halin da ake ciki mazauna garin na Jowhar na tattara ya nasu ya nasu suna ficewa daga garin domin tsira da rayukan su. A tsawon watannin da suka gabata, garin mogadishu na fuskantar ɗauki ba daɗi tsakanin mayaƙan Islama da madugan yaƙi dake da goyon bayan Amurka. Kimanin mutane 350 ne suka rasa rayukan su a tarzomar data ɓarke a ƙasar watanni uku da suka gabata.