Ana ci gaba da samun tashin hankali a Libiya | Labarai | DW | 22.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da samun tashin hankali a Libiya

Masu zanga zanga sun nemi kawo karshen rikicin da ke faruwa a garin Bani Walid na Libiya.

Masu zanga zanga sun kutsa majalisar dokokin ƙasar Libiya, a wannan Lahadin da ta gabata, inda su ke neman ganin ɗaukan matakan shawo kan rikicin garin Bani Walid, inda ake ɗauka tungar hamɓararren Shugaba Marigayi Mu'ammar Gaddafi.

Masu ɗauke da makamai daga Misrata da ke da alaƙa da ma'aikatan tsaro, sun kai harin birnin mai jama'a 70,000, da ya hallaka mutane 22, tare da jikata fiye da mutane 200.

Sabbin mahukuntan ƙasar ta Libiya sun gudanar da zaɓe, amma har kawo yanzu babu cikekken doka da oda, shekara guda bayan kawar da gwamnatin Marigayi Gaddafi ta Shekaru 42.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas