Myanmar: Ana ci gaba da aiwatar da kisan kare dangi
October 25, 2018Talla
Marzuki Darusman wakilin majalisar a kasar, ya ce matsalar babba ce, kuma har yanzu dubban 'yan Rohingya ne ke tururuwa suna tserewa gidajensu bisa wannan barazana da suke fuskanta, wadanda suka zabi zama kuwa suna fuskantar matsaloli na musgunawa da kaskanci daga jami'an gwamnati inji sanarwar.
A wani taron manema labarai, mista Darusman ya ce, ba a daina aikata laifi na kisan kare dangi ba akan 'yan tsirarun da ke zaune a jahar Rakhine a arewacin kasar. Amma Jakadan Myanmar a Majalisar Dinkin Duniyan, Hau Do Suan, ya karyata sakamakon wannan binciken inda ya ce an nuna bangaranci da rashin adalci ga gwamnatin Myanmar. Dubban 'yan kabilar Rohingya ne suka rikide zuwa 'yan gudun hijira bayan da kazamin rikicin kabilanci ya barke a kasar.