1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da kaiwa juna hare hare tsakanin Isra´ila da Hezbollah

July 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuqQ
Har yanzu babu alamun kawo karshen hare haren da Isra´ila ke kaiwa a cikin Libanon. Majiyoyin asibiti sun ce akalla fararen hula 10 aka kashe a wani hari da helikoptan yakin Isra´ila ya kai kan wata safa dauke da mutane dake tserewa daga wani kauye dake kudancin Libanon. A kuma halin da ake ciki kungiyar Hezbollah na ci-gaba da harba rokoki cikin arewacin Isra´ila. Jami´ai sun ce rokoki biyar sun afkawa wata unguwa amma ba wanda ya jikata. Tun da sanyin safiyar yau sojojin Isra´ila 4 sun bata bayan wani hari da aka kai a gabar ruwan Libanon ya lalata wani jirgin ruwan yakin Isra´ila. A kuma halin da ake ciki ministan kula da ´yan kakagida Seev Boim ya ce Isra´ila ta kuduri aniyar halaka shugaban Hezbollah a Libanon Hassan Nasrallah. Ministan ya ce sojojin Isra´ila zasu bad da Nasrallah da zarar sun samu damar yin haka.