Ana ci gaba da kai kayan agaji a Siriya | Labarai | DW | 22.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da kai kayan agaji a Siriya

Majalisar Dinkinj Duniya ta ci gaba da kai kayan agaji a yankunan da ke birnin Aleppo jim kadan bayan da kazamin fada ya hana ci gaba da kai hare-hare daga dukkanin bangarori da ba sa ga maciji da juna.

Babban jami'in asibitin al-Quds Dr. Hamza al-Khatib ya tabbatar da mutuwar mutane 45 a wani harin bama bamai ta sama da aka kai a sansanin 'yan tawaye da ke birnin Aleppo. A farkon wannan makon madai anzargi jiragen yakin na dukkanin bangarorin da je jagorantar yaki a Siriya da kai hari kan motocin dakon kayan agaji dake wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 ciki har da wani jami'in agaji na Red Cross.

To sai dai jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Siriya RAMZY Ezzeldin akwai kyakkyawar fatan sake zaman sulhun dan kawo zaman lafiya nan gaba, to amma shugaban kasar Siriyan Bashar al-Assad na ganin hannu da sauran manyan kasashen duniya ke da shi a rura wutar rikici ke hana cimma tsagaita wuta a kasar.

"A shirye muke da ko wace irin tattaunawa da zai tabbatar da zaman lafiya a Siriya, to amma kasashen Amirka da sauran kasashen kamar saudiya da ke maramata baya basa da niyar ganin ankawo karshen murza wuta a Siriya."