Ana ci-gaba da kai hari a kan ´yan shi´a a Iraki | Labarai | DW | 17.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da kai hari a kan ´yan shi´a a Iraki

Akalla mutane 16 aka kashe sannan kimanin 60 sun jikata a jerin hare hare da aka kai a ciki da kuma kewayen babban birnin Iraqi, Bagazada. Daya daga cikin hare haren da su ka fi muni ya auku ne a cikin wata kasuwa dake cike da jama´a a tsakiyar birnin Bagadaza. Kamar yadda hukumomi suka nunar mutane 5 suka rigamu gidan gaskiya a fashewar wani bam a cikin kasuwar. A wani harin roka da shi ma aka kai kan wata kasuwa dake wata unguwar ´yan shi´a mutane 2 sun rasu. Sannan sama da mutane 9 ciki har da sojojin Iraqi aka halaka a hare hare guda biyu da aka kai kan wani wurin binciken ababan hawa. Ana ci-gaba da kai munanan hare hare a cikin babban birnin na Iraqi duk da tsauraran matakan tsaro da aka kaddamar a birnin a ranar laraba da ta wuce.