Ana ci gaba da gumurzu a birnin Aleppo da kewaye | Labarai | DW | 11.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da gumurzu a birnin Aleppo da kewaye

Sau da yawa an ji karar hare-haren gurnati atileri lokacin tsagaita wuta tsawon awoyi uku kowace rana.

Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a Aleppo duk da sanarwar da Rasha ta bayar game da tsagaita wuta tsawon awoyi uku kowace rana don bada damar kai kayan agaji ga mabukata. Rahotanni sun ce sau da dama tun bayan fara tsagaita wutar, an kai hare-haren gurnati a yankunan 'yan tawaye da ke Aleppon. Shi ma ofishin sa ido kan hakin dana Adam a Siriya ya tabbatar da dorewar tashin hankalin. A ranar Laraba Rasha ta sanar cewa daga wannan Alhamis za a dakatar da fadan ciki har da harin makaman atileri da jiragen saman yaki daga karfe 10 zuwa karfe daya agogon Siriya, don amfani da wannan tsukin lokacin wajen kai agajin jin kai ga al'ummar Aleppo da ke cikin mawuyacin hali sakamakon yakin.