Ana ci gaba da gudanar da zaben Ghana | Labarai | DW | 08.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da gudanar da zaben Ghana

Da safiyar wannan Asabar rana ta biyu, ake ci gaba da gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisun kasar Ghana wanda aka tsaiwaita

Da safiyar wannan Asabar rana ta biyu, ake ci gaba da gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisun kasar Ghana wanda aka tsaiwaita, cikin yankunan kasar da aka samu matsaloli na'urorin aiki, da su hana dubban mutane gudanar da zaben a jiya Jumma'a.

Wannan mataki na hukumar zaben kasar, ya samu karbuwa daga daukacin jam'iyyun siyasan kasar, kuma ana kyautata zaton kasar da ke yankin yammacin Afirka, za ta ci gaba da rike martabanta na gudanar da zabe cikin tsanaki da kwanciyar hankali.

Ana saran za ayi fafatawa mai zafi tsakanin Shugaba John Dramani Mahama, da dan takarar babbar jam'iyyar adawa Nana Akufo-Addo.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas