Ana ci gaba da gudanar da zaɓe a Yuganda | Siyasa | DW | 18.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana ci gaba da gudanar da zaɓe a Yuganda

Al'ummar ƙasar Yuganda na ci gaba sa gudanar da zaɓen Shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokokin ƙasar, har a yau Jumma'a cikin wani hali na tashin hankali

Rahotanni da ke fitowa daga ƙasar na cewar mafi yawancin al'ummar ƙasar ta Yuganda sun koka game da tsaikon fara zaɓen kan lokaci da rarraba kayan zaɓen a wasu sassan musamman manyan biranen ƙasar,hakan dai ya janyo dogayen layika a yawancin mazaɓun inda al'umma ke cewa sai sun ga ƙwal uwar daka wato babu gudu babu jada baya sai sun zaɓi ra'ayinsu.

An samu tsaiko wajen gudanar a zaɓen a cibiyoyi da dama na zaɓen

Sai dai daga bisani humar zaɓen ƙasar ta fito ta ba da hakuri game da tsaikon raba kayan aiki dama fara zaɓen kan lokaci.Kiyaliya complaint wata wadda ta je kada ƙuri'a ce ta bayyana damuwar a game da isar kayan zaɓen a makare inda ta bayyana cewar."Da gangan aka ƙi kawo kayan zaɓen kan lokaci kuma ba mu katun zaɓemu ba kan lokaci saboda haka babu damar in amfani da nawa wajen yin zaɓe".Haka kuma Al'ummar sun nuna damuwarsu matiƙa gaya game da yadda aka yanke kafafen sadarwa na zamani irinsu Facebook da Twiter a dai dai lokacin da ake gudanar da zaben gadan-gadan

Tashin hankali ya ɓarke a lokacin zaɓen

A ɓangaren Jami'an tsaron ƙasar ta Yuganda a birnin Kamfala sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan gungun wasu masu kaɗa ƙuri'a waɗanda aka zarga da yinƙurin tada zaune tsaye game da tafiyar da zaɓen.Shugaban ƙasar da ke kan karagar mulki Yoweri Museveni na fuskantar matsin lamba daga babban abokin hamaryarsa Kizza Besigye. Sai dai 'yan sandan ƙasar ta Yuganda sun cafke shi madugun 'yan adawan ƙasar Besigye bisa zargin da ake yi masa na tafka magudin zaɓe. jam'iyyar ta FDC ta ce ba ta san inda jami'an tsaro suka kaishi ba.

Sai dai Da yake magana da manema labaru jim kadan bayan ya kada ƙuri'a kuma kafin a kamashi, babban abokin hamaryar Kizza Besgye ya ce kwata-kwata zaɓen babu alamun adalci cikinsa yana mai cewa.Wasu ƙungiyoyi dai na zargin shugaban da san dauwama kan karagar mulkin ƙasar yayin da kuma ake ƙara zarginsa da yin amfani da jami'an tsaro wajen ƙuntatawa 'yan adawa.

Sauti da bidiyo akan labarin