1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lamura sun turnuke a wasannin lig na kasashen Turai

Mouhamadou Awal Balarabe SB
September 16, 2024

Libya ta yi abin kai a gasar futsal ta duniya yayin da Angola ta yi abin fallasa, Su kuwa 'yan mata Amurka sun yi wajen road da na Jamus a gasar duniya ta kwallon mata 'yan kasa da shekaru 20.

https://p.dw.com/p/4kgZ0
Holstein Kiel - Bayern München
Bundesliga wasa tsakanin Holstein Kiel da Bayern MünchenHoto: Gregor Fischer/dpa/picture alliance

 

Kasashen da ke wakiltar nahiyar Afirka a gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa ta futsal da ke gudana a Uzbekistan sun shiga fagen fafatawa, inda a wasanta na farko Libya ta yi nasara a kan New Zealand da ci 3-1. Wannan dai shi ne karon farko da Libya ke samun nasara a gasar cin kofin duniya ta Futsal, kuma ita ce ke kan gaba a rukuninta na hudu da maki uku yayin da Spain da kazakstan ke biya mata baya da mai day-daya. Sai dai a nata bangare, Angola ta dibi kashinta a hannun Afghanistan da ta doke ta da ci 6-4. Tun daga mintunan farko ne Angola ta samu kanta a cikin kunci, lamarin da ya bai wa Afganistan fara zazzaga kwallo tun minti na biyu da fara wasa. Ita dai Angola tana a matsayi na uku a rukuninta na uku a bayan Ajentina mai maki uku da Afghanistan ita ma mai maki uku. A wannan Litinin ne Maroko da ke zama zakaran Afirka na futsal ke karawa da Tajikistan a wasan farko a rukuni na biyu da ke hada ta da Panama da Potugal.

Tun bayan fara gasar farko a shekarar 1989 a Netherlands, ana gudanar da gasar kofin duniya ta futsal duk bayan shekaru hudu tun daga 1992 a cikin makonni biyu a tsakanin kasashe 24 na duniya. Kuma bayan wasan rukuni, kungiyoyin biyu na farko a kowace rukuni da kuma kasashen 4 da ke samun kyakkyawan matsayi na uku ne ke hayewa zuwa mataki na gaba. A yanzu dai, Potugal ce ke rike da kofin duniya na futsal da ake gudanarwa a rufeffen filin wasa.

Fußball WM der Frauen 2019 | England - USA
Hoto: John Walton/PA Wire/empics/picture alliance

A ci-gaba da gudanar da wasanni neman lashe kofin kwallon kafa na duniya na mata 'yan kasa da 20 da haihuwa da ke gudana a Kolombiya, an kai matsayi kusa da kusa da na karshe na quater final bayan da aka yi waje road da daukacin wakilan Afirka ciki har da 'yan matan Najeriya da kuma Kamaru da Ghana. A yanzu haka ma babban abin mamakin, shi ne 'yan matan Koriya ta kudu suka yi nasarar lallasa zakakuran 'yan matan Brazil da ci daya mai ban haushi. haka su ma 'yan matan Japan sun shammaci takwarorinsu na Spain da ci daya mai ban haushi. Amma a karawa da aka yi tsakanin Holland da Kolombiya mai masaukin baki, sai da aka kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida tukunin 'yan matn Netherland suka yi wajen road da 'yan kolombiya. Haka lamarin da ya wakana tsakanin 'yan matan Amurka da na Jamus, inda ci 2-2 bayan busan karshe ya kai su ga bugun fenarti, amma a karshe 'yan USA suka samu nasara ci 3-1 a kan takwarorinsu na Jamus.

Ranar Laraba mai zuwa ne za a fara wasanin kusa da na karshe na neman cin kofin mata 'yan kasa da 20 da haihuwa, inda 'yan matan Amurka za su kara da 'yan Koriya ta Kudu, yayin da a ranar Alhamis 'yan matan Koriya za su yi wasansu da na Holland

Holstein Kiel - Bayern München
Bundesliga wasa tsakanin Holstein Kiel da Bayern MünchenHoto: Gregor Fischer/dpa/picture alliance

A nan gida Jamus, an gudanar da wasannin mako na uku na gasar kwallon kafa ta Bundesliga a karshen mako, inda kungiyoyi suka zura kwallaye talatin da biyar (35) a wasanni 9 da aka buga. Hsali ma dai, bakwai daga cikin kwallayen sun samu ne a filin wasa a Kiel da ke arewacin Jamus, inda Yaya-babba Bayern Munich ta bi sabon shiga Holstein Kiel har gida, kuma ta lakaba mata dan karen duka ci 6-1 ciki har da kwallaye uku da Harry Kane ya ci. Amma Marcel Rapp da ke zama kocin Holstein Kiel ya ce wannan cin mutunci ya samu ne sakamakon rashin maida hankali yayin wasan daga bangaren wadanda yake horaswa:

"Mun tafka kurakurai da yawa a farko-farkon wasan, saboda haka ne ba mu iya sake samun damammaki ba kwata-kwata. Hare-hare kalilan kawai muka kai a wasan, sannan kwallon da muka zura wa gidanmu ya yi mummunan tasiri a kanmu baya ga matsa kaimi da Bayern ta yi mana. A gaskiya abu ne mai wuyar karewa."

Ita ma Bayer Leverkusen da ke rike da kambun zakara na kwallon kafar Jamus ta taka rawar ganin inda ta doke Hoffenheim da ci 4-1. Godiya ta tabbata ga dan wasan gaba dan asalin Najeriya Victor Boniface da zura kwallaye biyu a ragar abokan hamayya, makonni biyu bayan Leverkusen ta sha kashi a mako na biyu. Wannan nasarar ta kara wa Xabi Alonso, kocin Bayer Leverkusen kwarin gwiwa na sake ganin badi.

"Kowane wasa na da mahimmanci, wannan tabbas ne. Mun nuna cewa muna da fikirar yin wasa mai kyau, kuma ina tsammanin mun cancanci wannan nasarar. Amma akwai gyara a wasanni na gab domin ma mintuna 10 kafin a je hutun rabin lokaci, akwai abubuwa da ya kamata mun inganta. Amma a jimilce, mun yi kyakkyawan aiki, abin da muke bukata shi ne ci gaba kuma wannan ita ce hanya madaidaiciya don ci gaba."

Bundesliga | SC Freiburg - VfL Bochum | Junior Adamu
Bundesliga wasa tsakanin SC Freiburg da VfL BochumHoto: Memmler/Eibner-Pressefoto/picture alliance

A sauran sakamakon wasannin Bundesliga kuwa, Leipzig ta yi tuntube a gida a hannun Union Berlin da ci 0-0 bayan nasara biyu a jere. Amma kasancewar tana da  maki bakwai, tana a matsayi na uku teburin Bundesliga a bayan Bayern Munich da Borussia Dortmund. Hasali ma, Yaya-karama Dortmund ta yi nasarar lallasa Heidenheim da ke a matsayi na hudu da ci 4-2. Ita kuwa Eintracht Frankfurt ta samu nasara a kan Wolfsburg da ci 2-1, yayin da Stuttgart ta bi Borussia Monschengldbach har gida kuma ta doke ta da ci 3-1. A nata bangaren Freiburg ta doke Bochum da ci 2-1, yayin da Augsburg ta mamaye 'yar auta St Pauli da ci 3-1. Ita kuwa Mainz ta baras da damarta a gida inda Bremen ta shammace ta da ci 2-1.

Har yanzu dai muna fannin kwallon kafa, inda a manyan lig-lig na kasashen Turai ma aka taka leda:

A Ingila, Arsenal ta samu nasara a derby na arewacin London a kan Tottenham da ci daya mai ban haushi (1-0) a ranar Lahadi, lamarin da ya bta damar komawa matsayi na biyu a teburin gasar Premier. Sannan a yanzu maki biyu ne ke tsakaninta da Manchester City, wacce ta kasance babbar abokiyar hamayyarta kuma abokiyar karawarta ta gaba. Hasali ma, Manchester City ta lallasa Brentford da ci 2-1, yayin da Aston Villa ta mamaye Everton da ci 3-2. Ita kuwa Nottingham Forest ta shammaci Liverpool a gida da ci daya mai ban haushi, yayin da ita Newcastle ta bi Wolves har gida kuma ta doke ta da ci 2-1.

Spanien | La Liga inda aka kara tsakanin Sevilla da Celta
La Liga na Sifaniya wasa tsakanin Sevilla da Celta Hoto: CordonPress/IMAGO

A Spain, FC Barcelona da ta samu nasara ta biyar a wasanni biyar ta hanyar doke Girona da ci 4-1, inda ta samu taimakon zakarun Turai Lamine Yamal da yi zuwa kwallaye biyu da kuma Dani Olmo da Pedri. A yanzu dai kungiyar ta yankin Catalania ce ke saman teburin La Liga, yayin da Real Madrid ke a matsayi na biyu bayan da ta bi Real Sociedad gida kuma ta doke t da ci 2-0.  Ita lkuwa Atletico Madrid ta yi wa Valencia dukan kawo wuka ci 3-0, lamarin da ya sa ta samun maki 11 da matsayi na uku a saman teburin gasar Spain, yayin da Celta Vigo take ci gaba da jan zarenta ta hanyar sake samun nasara a gida 3-1 a gaban Valladolid. A nata bangaren, Athletic Bilbao ta doke Las Palmas da ci 3-2, duk da cewa an kori daga daga cikin 'yan wasanta daga fagen dage.

A Italiya: A karon farko cikin shekaru biyu, Napoli ko Naples ta samu nasara ta uku a jere 4-0 a gaban Cagliari, lamarin da ya sa ta samun matsayi na farko a Serie A bayan tuntube da Inter Milan da ke rike da kambun zakara ta yi inda ta tashi 1-1 a karawar da ta yi da Monza. Ita ma Juventus Turin ta yi canjaras da Empoli (0-0), haka kuma irin wannan samakamo aka samu a wasan da aka yi tsakanin Torino da Lecce (0-0). Amma Atalanta Bergamo ta koma matsayi na 8  da maki shida ta hanyar lallasa Fiorentina da ci 3- 2.

'Yan wasan Najeriya lokacin gasar neamn cin kofin Afirka a Cote d'Ivoire
'Yan wasan Najeriya lokacin gasar neamn cin kofin Afirka a Cote d'IvoireHoto: Franck Fife/AFP/Getty Images

A Najeriya, tun bayan da Bruno Labbadia ya ki amincewa da zama kocin Najeriya, ake ci gaba da jiran ganin wanda hukumar NFF za ta nemo domin horas da Super Eagles wanda a wasannin da Najeriyar ta fafata na neman gurbi a gasar cin kofin kasashen Afirka, Augustine Eguavoen ne ya jagoranci kasar na wucin gadi. Bisa ga tarihi dai, ba a taba samun lokaci da masu horaswar na gida da waje suke kin amsar tayin da ake musu ko kuma jinkiri wajen samar da mai horaswa kamar wannan ba, duk da kwararrun 'yan wasa da Najeriya ta mallaka.

Daruruwan 'yan kasar Yuganda da fitatten 'yan wasa sun halarci jana’iza a ranar Asabar na yar wasan yar kasar Yuganda Rebecca Cheptegei da abokin zamanta dan kasar Kenya ya kona ta. Sai dai Kipchumba Murkomen da ke zama sakataren ministan harkokin wasanni na Kenya, ya sanar da cewa an dauki matakan kawar da irin wannan mummunan cin zarafi a fannin motsa jiki, inda ya ce ma'aikatarsu ta tuntubi ma’aikatar cikin gida da ma’aikatar kula da daidaiton jinsi don kafa layin wayar tarho kyauta inda ‘yan wasa za su iya tuntuba idan suna fusakntar barazanai. Idan za a iya tunawa dai, Rebecca Cheptegei ta rasu ne a ranar 5 ga watan Satumba bayan da saurayinta  mai shekaru 32, ya zuba mata fetur jiki kuma ya banka mata wuta.