Ana ci gaba da binciken dalilan faduwar jirgin saman Rasha a Masar | Labarai | DW | 04.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da binciken dalilan faduwar jirgin saman Rasha a Masar

'Yan sanda hudu sun hallaka sakamakon harin tsageru a yankin Sinai na Masar da ake binciken dalilan hadarin jirgin saman kasar Rasha.

Wani harin bam da kungiyar IS mai neman kafa daular Islama ta dauki alhakin kaiwa ya hallaka 'yan sanda hudu a yankin Sinai na kasar Masar, yayin da masu bincike ke neman dalilan da suka janyo faduwar jirgin saman kasar Rasha dauke da mutane 224.

Kawo yanzu kungiyar ta IS wadda ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman ta gaza ba da wasu shaidu da za su tabbatar da haka. Jirgin saman ya yi hadari lokacin da ya taso daga garin Sharm al-Sheikh na yawon shakatawa a kan hanyar zuwa birnin St Petersburg na Rasha. Tuni mahukuntan Masar suka karfafa matakan tsaro musamman filayen jiragen saman kasar.

A wannan Laraba Shugaba Abdel-Fattah al-Sissi na kasar ta Masar ke fara ziyarar aiki a birnin London na Birtaniya.