Ana ci gaba da aikin ceto bayan haɗarin mahaƙa a Turkiya | Labarai | DW | 14.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da aikin ceto bayan haɗarin mahaƙa a Turkiya

Jami'an tsaro a Turkiya sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye a kan masu zanga-zangar nuna fushinsu ga haɗarin da ya auku a wata mahaƙar kwal ta ƙasar.

'Yan sanda a birnin Ankara na ƙasar Turkiya sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye da feshin ruwa a kan daruruwan masu zanga-zanga biyo bayan haɗarin da ya auku a wata mahaƙar kwal da ke yammacin ƙasar. Masu zanga-zangar sun yi ta jifar jami'an tsaron da duwatsu kana sun yi ta rera waƙoƙin adawa da gwamnati. Gungun masu zanga-zangar sun so yin maci ne daga jami'ar babban birnin ƙasar ta Turkiya zuwa ma'aikatar makamashi. A kuma halin da ake ciki ƙasashe da yawa ciki har da Jamus da Girika da kuma Isra'ila sun yi wa Turkiya tayin taimako wajen aikin ceto a haɗarin da ya auku a mahaƙar ta ma'adanai. Shugaban tarayyar Jamus Joachim Gauck da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun nuna kaɗuwa kana sun aike da sakon jaje ga ƙasar ta Turkiya. Paparoma Francis kira ya yi da a yi wa waɗanda haɗarin ya rutsa da su addu'a. Mutane fiye da 200 ne suka rasa rayukansu a haɗarin. Tuni dai hukumomin Turkiya suka ayyana zaman makoki na kwanaki uku.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane