Ana ci gaba da aikata ta′asa a Afirka ta Tsakiya: Amnesty | Siyasa | DW | 11.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana ci gaba da aikata ta'asa a Afirka ta Tsakiya: Amnesty

Kungiyar ta kare hakkin dan Adam ta ce rashin gudanar da cikakken bincike kan aikata laifukan yaki yana kara rura wutar rikicin kasar.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta fitar da rahoto kan take hakkin mutane da ake samu a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Rahoton ya fito fili da hakikanin abin da ke faruwa a kasar.

Rahoton na kungiyar Amnesty ya nuna yadda aka samu kyakkyawar fata kan kare fararen hula da kawo karshen nuna son kai, lokacin da aka tura dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumba na wannan shekara ta 2014.

Amma lamura sun sauya wata guda bayan tura dakarun inda aka samu tashe-tashen hankula a birnin Bangui fadar gwamnatin kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da wasu sassan kasar.

Christian Mukosa da ke zama mai bincike kan harkokin kungiyar Amnesty a birnin Dakar na kasar Senegal yana cikin wadanda suka rubuta rahoton kan kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

"Abin da za a ce rahoton ya kunsa shi ne ana ci gaba da take hakkin dan Adam, da aikata laifukan yaki, da kuma cin zarafin mutane. Tun shekara ta 2013 abin ke karuwa saboda rashin hukunta wadanda ake zargi. Shi ya sa wasu ke ci gaba da aikata irin wannan ta'asa, bisa rashin hukunci a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya."

Muhimmancin rahoton Amnesty International

Wannan rahoto na Amnesty International ya mayar da hankali kan shekarar da ta gabata ta 2013 zuwa wannan shekara ta 2014, ya kuma nuna yadda kungiyoyi kamar Anti-Balaka da Seleka ke ci gaba da bijire wa dokoki wajen aikata miyagun laifuka, duk da saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Brazzaville na kasar Kwango tare da kungiyoyin addinai da fararen hula.

Christian Mukosa ya yi karin haske kan muhimmancin fitar da wannan rahoto:

"Wannan rahoto ne da ya kunshi abin da ke faruwa a wannan shekara kuma a watan Yuli mun wallafa sunayen wadanda ake zargi da ayyukan cin zarafi na kungiyoyin anti-Balaka da Saleka. Suna kona kauyuka, da saka yara ayyukan soji, da yi wa mata fyade gami da tilasta wa mutane gudun hijira."

Wani abin da ke kara tabarbara lamaru shi ne rashin hukunta masu aikata laifuka, inda Anmesty ta yi nuni da rahoton kwararru na Majalisar Dinkin Duniya ya wanda tabbatar da cewa mutanen da ake zargi suke ci gaba da haddasa ta'asa.

Hukunta duk mai hannu a ta'asa

Wani abu da rahoton ya kunsa shi ne maganar dakarun kasar Cadi wadanda ake zargi da hannu wajen take hakkin dan Adam, amma kuma gwamnatin kasar ta Cadi ta janye dakarun daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Christian Mukosa na kungiyar Amnesty ya yi karin haske kan batun:

"Rahoton ya nuna cewa dakarun na Cadi zuwa watan Afrilu ana zarginsu da aikata laifukan take hakkin dan Adam. Kuma za mu ci gaba da neman ganin mahukuntan Cadi sun gudanar da bincike domin hukunta duk wanda yake da laifi ko da sun kama kasarsu ta Cadi."

Rahoton ya nuna karara cewa babu wata manufa ta siyasa domin kawo karshen aikata miyagun laifuka a kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Sauti da bidiyo akan labarin