Ana bukatar sabuwar koyarwar addini | Labarai | DW | 23.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana bukatar sabuwar koyarwar addini

Babban limamin jami'ar Azhar da ke kasar Masar ya yi kira da a sabunta manhajar koyarwar addinin Musulunci don yaki da tsattsauran ra'ayi.

Babban limamin jami'ar Azhar ta kasar Masar Sheikh Ahmed al-Tayib ya fada wa wani babban taron yaki da ta'addanci a kasar Saudiyya cewa ya kamata a yi wa tsarin koyarwar addinin Musulunci garambawul. A jawabin bude taron a birnin Makka, Sheikh Ahmed al-Tayib ya yi nuni da cewa bisa tarihi akwai tarin kura-kurai na fassara cikin addinin da suka janyo tsauraran akidoji da ra'ayoyi tsakanin Musulmi. Yanzu haka dai manya-manyan malamai na ci gaba da taron na yini uku a Makka a kan yaki da ta'addanci a cikin addinin Musulunci. Sheikh Al-Tayib ya ce dole Musulmi su samu sabon hadin kai da zamanantar da koyarwar addini wanda kuma zai nuna karin juriya. Ya ce da haka ne kawai za a iya dakushe kyamar da ake nuna wa addinin Musuluncin a nahiyar Turai.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu