Ana bikin tunawa da kashe Ken Saro-Wiwa | Labarai | DW | 10.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana bikin tunawa da kashe Ken Saro-Wiwa

Shekaru 20 bayan zartar da hukunci kisa kan Ken saro-Wiwa har yanzu 'yan yankin Niger Delta na Najeriya na fama da matsalar gurbata muhalli da ya yi fafutuka a Kai.

A wannan Talatar ce ake gudanar da bikin zagayowar shekaru 20 da zartar da hukunci kisa a kan marubuci kana fitaccen dan gwagwamayar nan na yankin Niger Delta wato Ken Saro-Wiwa. Wannan biki da ke gudana a birnin Bori na yankin Ogoni ya kunsha addu'o'i da kuma wakokin baka.

A zamanin mulkin Sani Abacha ne aka yanke wa shugabannin al'ummomi guda tara na yankin Ogoni mai arzikin mai ciki har da Saro-Wiwa hukunci kisa bisa laifin kashe wasu jiga-jigan yakin Ogoni. Sai dai aiwatar da hukunci a ranar 10 ga watan Nuwamba ya janyo suka daga kasashen duniya, lamarin da ya sa aka dakatar da Najeriya daga kungiyar kasashe rainon Ingila ta Commonweath na tsawon shekaru hudu.

Sai dai kuma shekaru 20 bayan aiwatar da hukunci akan mutumin da yake fafutukar kwato musu 'yanci, har yanzu ana cigaba da fuskantar matsalar gurbta muhalli da rashin ruwa mai tsafta a yankin na Ogoni.