Ana bazartar da arzikin gabashin Afirka | Labarai | DW | 17.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana bazartar da arzikin gabashin Afirka

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabuwe shi ne ya bayyana haka a taron Ƙungiyar SADEC ta ƙasashen gabasin Afirka da ake yi a Victoria Falls.

Shugaba Robert Mugabe ya yi kira ga shugabannin ƙasashen gabasin Afirka da su ƙara azama, wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasashensu, ta hanyar fitar da hajjojin da aka kammala ƙerawa daga ƙasashen zuwa waje,saɓannin yadda ake fitar da albarkatun na ƙarƙashin ƙasa waɗanda ba a tace ba.

Mugabe wanda ke yin jawabi a bikin buɗe taron shugabannin ƙasashen gabashin Afirka na Ƙungiyar SADEC a yammancin Victoria Falls da ke a Zimbabuwe ya ce yin hakan bai dace ba.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu