Ana aikata laifin yaki a arewa maso gabacin Najeriya - Amnesty | Siyasa | DW | 31.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana aikata laifin yaki a arewa maso gabacin Najeriya - Amnesty

Hare-haren da Boko Haram ke kaiwa da mummunan martani da dakarun tsaron Najeriya ke mayarwa sun yi muni a watanni ukun farko na shekarar 2014.

Karuwar yawan hare-hare da kungiyar nan da ake wa lakabi da Boko Haram ke kaiwa da kuma zazzafan martanin da dakarun tsaron Najeriya ke mayarwa sun sa a watanni ukun farko na wannan shekara, yawan mutanen da aka kashe a yankin arewa maso gabacin tarayyar Najeriya ya haura 1,500, kuma fiye da rabinsu fararen hula ne. Wannan dai na kunshe ne a cikin rahoton da kungiyar kare hakin dan Adam ta Amnesty Inernational ta wallafa bayan bincken da ta yi a kan tashe-tashen hankulan na arewa maso gabacin Najeriyar.

Amnesty International ta ce munin da rikicin ya yi a yankin arewa maso gabacin Najeriya a wannan shekara ta 2014, ya rikide zuwa wani rikicin daukar makami na cikin gida inda dukkan masu ruwa da tsaki a rikicin ke karya dokokin kasa da kasa dangane da kare hakin dan Adam, kana ana aikata laifin yaki a hare haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa da martanin da dakarun tsaron Najeriya ke mayarwa.

Yawan salwantar rayuka sakamakon munin rikici

Makmid Kamara shi ne mai bincike kan nahiyar Afirka a kungiyar ta Amnesty International ya yi karin haske.

"Yawan hare-hare ko zargin yi wa mutane kisan gilla ba tare da sun gurfanar gaban kotu ba saboda zarginsu da kasancewa 'yan Boko Haram, mutuwar mutane a hannun 'yan sanda da hari kan fararen hula da lalata matsugunan wadanda ba su ji ba su gani ba. Wadannan abubuwa ne da kotun kasa da kasa ta lissafa a jerin laifukan yaki. A ganinmu wadannan laifuka ne da dakarun gwamnati da kuma 'yan Boko Haram suka aikata a Najeriya."

Kungiyar ta ce salwantar rayuka sama da 1500 a cikin wata uku na nuni da matukar munin halin da ake ciki. Ta ce gamaiyar kasa da kasa ba za ta ci gaba da kawar da ido daga wannan ta'asa ba, wadda Amnesty din ta ce ya fi shafar fararen hula. Kungiyar ta ce fiye da rabin mutane 1500 ciki har da 'yan makaranta da aka kashe a rubu'in farko na wannan shekara a rikicin na arewa maso gabacin Najeriya, 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne suka aikata.

Bayanai game da samun manyan kaburbura

Hakazalika Amnesty ta ce bayanan da ta samu sun nuna cewa sama da mutane 600 dakarun tsaro suka kashe a Maiduguri a ranar 14 ga watan Maris, bayan harin da 'yan Boko Haram suka kai kan wani barikin soji da ke birnin, inji Makmid Kamara.

"Wasu bayanan da muka samu sun nuna cewa yawan wadanda aka kashe zai iya zarta wanda muka wallafa. Mun samu hotuna da faifayen bidiyo da bayanai daga shaidun ganin ido na mutane da aka binne a manyan kaburbura. Sannan hotunan kumbon sattelite da muka samu sun tabbatar da manyan kaburburan da dakarun tsaron Najeriya suka binne mutanen da aka kashe a ranar 14 a wata Maris."

Fahndungsfoto Abubakar Shekau

Hoton neman shugaban Boko Haram Mallam Abubakar Shekau

Ko da yake Amnesty ta aike wa hukumomin Najeriya da wasikar game da wannan zargin, amma kasancewa Najeriyar tana jan kafa wajen gudanar da bincike ko gurfanar da masu laifin a gaban shari'a, kungiyar ta yi kira ga hukumar tarayyar Afirka da kuma Majalisar Dinkin Duniya da su taimaka wa Najeriya gudanar da bincike a kan aikace-aikacen da ka iya zama laifukan yaki da kuma keta hakin dan Adam, inji Makmid Kamara mai bincike kan Afirka a kungiyar ta Amesty International.

"Bisa tarihi Najeriya ba ta gudanar da sahihin bincike na zargin da ake wa jami'an tsaronta. An sha kafa kwamitocin bincike amma a karshe ba a aiki da rahotanni da kuma shawarwarin da suka bayar. Saboda haka muke kira ga mahukuntan Najeriya da su hada kai da gamaiyar kasa da kasa don gudanar da sahihin bincike kan wannan ta'asar."

Amnesty ta yi kira ga kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS da kuma Majalisar tsaro da zama lafiya ta Afirka da su duba rikicin na arewa maso gabacin Najeriya tare kuma da ba da gudunmawa don kawo karshen cin zarafin farar hula.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin