1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zartar da shari'ar Sanusi Lamido Sanusi

April 3, 2014

Kotu a jihar Lagos ta bukaci gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta biya tsofon gwamnan babban bankin kasar diyyar cin zarafi da keta haddin da ta yi masa.

https://p.dw.com/p/1BbZB
Hoto: Reuters

Yau ne wata kotu a birnin Lagos ta fitar da sakamakon shari'ar da ta gudanar, kan karan da tsofon Gwamnan babban bankin Tarayyar Najeriya Sanussi Lamido Sanussi ya shigar a gabanta.

Mai shari'a Justice Ibrahim Uba, ya tabbatar da cewa an ci zarafin Tsofon Gwamnan babban bakin Tarayyar ta Najeriya Sanusi Lamido Sanusi, tare da neman gwamnatin kasar da ta rubuta masa takardar neman afuwa, sannan kuma ta biya shi diya ta cin zarafi sa da keta haddin sa da tayi, da kudi naira milian 50, sannan kuma ta mayar masa da Paspo din sa da ta karbe.

Saidai Lawya mai kare gwamnatin ta Najeriya Paden Ajegu yaki yace uffan kan wannan shari'a, wadda yake ganin zasu daukaka kara a kanta, yayin da Lawya mai kare Sanusi Lamido Sanusi Victoria Alonge, ta jinjinawa kotu bisa daukan matakan da tace ya dace kan wannan batu.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohamed Abubakar