An zartar da sabuwar doka kan baki a Faransa | Labarai | DW | 18.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zartar da sabuwar doka kan baki a Faransa

Majalisar dokokin Faransa ta amince da dokar tsaurara matakan shigi da fici a kasar, da aka dade ana tababa a kanta.

Dokar wacce zata zamowa baki dake son yin kaka gida a kasar ta Faransa kaya a makogoro, ta kuma bukace su dasu martaba tafarki na mulkin dimokradiyyar kasar tare kuma da koyan harshen faransanci.

Bugu da kari dokar za kuma ta haifarwa da bakin matsaloli na kawo iyalansu kasar don zama tare dasu.

Rahotanni dai sun nunar da cewa ministan kula da harkokin cikin gida kuma mutumin dake fatan darewa shugabancin kasar ta Faransa ne a nan gaba, wato Nicolas Sarkozy ya gabatar da wannan kuduri a gaban majalisar dokokin kasar.

Ya zuwa yanzu dai tuni jam´iyyun adawa da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasar suka yi Allah wadai da daukar wannan kuduri da cewa mataki ne na nuna wariyar launin fata.

Bayanai dai sun nunar da cewa kudurin sai ya sami amincewar majalisar dattijan kasar ne, san nan zai zama doka a kuma fara aiki da ita.