An zartar da hukuncin kisa a Texas ta Amirka | Labarai | DW | 07.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zartar da hukuncin kisa a Texas ta Amirka

Hukumomin jihar ta Texas sun zartar da hukuncin kisan a kan Juan Garcia dan shekaru 35 wanda kotu ta samu da aikata laifin kashe wani mutun a shekara ta 1998.

Hukumomin jihar Texas a Amirka sun zartar da hukuncin kisa kan wani mtun da kotu ta yanke wa hukuncin kisa bayan da ta same shi da aikata laikin sata tare da kashe wani mutun akan abin da bai wuce dala takwas na kudin Amirka ba a shekara ta 1998.

Kakakin hukumar gidan yarin ta birnin Texas ya bayyana cewa an zartar da hukuncin kisan a kan mutuman mai suna Juan Garcia dan shekaru 35 ta hanyar yi masa allurar mutuwa ta snadarin Letal da misalin karfe 11 da rabi da mintoci shida na daran jiya.

Wannan dai shi ne karo na tara da jihar ta Texas ta zartar da hukuncin kisa a cikin wannan shekara kawai, wanda ya dora jihar a sahun gaban jihohin kasar Amirka masu zartar da hukuncin kisa. Juan Garcia ya kuma kasance dan kaso na ukku da aka zartar masu da hukuncin kisa a wannan mako kadai a kasar ta Amirka.