An zargi Ukraine da laifin yin amfani da bam mai kwanso | Labarai | DW | 21.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi Ukraine da laifin yin amfani da bam mai kwanso

Ƙungiyar kare hakkin ɗan Adam ta Human Rights Watch ta ce sojojin Ukraine da kuma watakila dakarun 'yan aware masu goyon bayan Rasha sun yi amfani da makamin a yaƙin da suke yi.

A cikin wani rahoton da ta bayyana ƙungiyar ta ce ta ɗauki tsawon mako guda tana gudanar da bincike.Wanda a kansa ta ce ta gano cewar an harba bama-baman masu ya'ya har a kusan wurare 12 a Donesk waɗanda suka haddasa asarar rayuka da dama.

A shekarun 2010 Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana dokar haramta yin amfani da bama-baman masu ya'ya a lokacin yaƙi, sai dai Ukraine ba ta saka hannu ba a kan yarjejeniyar. Kawo yanzu sama da mutane dubu uku suka mutu a cikin tashin hankali na Ukraine.