An zargi sojin Najeriya da keta hakkin dan Adam | Labarai | DW | 14.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi sojin Najeriya da keta hakkin dan Adam

Majalisar Dinikin Duniya ta ce sojin Najeriya sun tafka laifuka na cin zarafin al'umma a yakin da suke yi 'yan kungiyar nan ta Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Babbar jami'ar hukumar kare hakkin bani adama ta Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay ce ta bayyana hakan a zantawar da ta yi da manema labarai dazu a Abuja, fadar gwamnatin tarayyar Najeriya.

Ms Pillay ta ce galibin mutanen da ta zanta da su a ziyarar da ta ke a kasar sun shaida mata cewa jami'an tsaron kasar na aikata laifuka na cin zarafin al'umma, wanda hakan ke kara rura wutar rikicin.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da al'ummar Najeriya ke cigaba da kokawa game da yadda tada kayar kayar baya a arewacin kasar ke dada munana, ko da dai a dan tsakanin nan rundunar sojin kasar ta ce ta karya kashin bayan masu tada zaune tsayen.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar