An zargi mayaƙan sa kai na Libiya da laifin cin zarafin bil adama | Labarai | DW | 30.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi mayaƙan sa kai na Libiya da laifin cin zarafin bil adama

Ƙungiyar kare hakin bil adama ta Amnesty International ta zargi ƙungiyoyin mayaƙan sa kai da ke ɗauke da makamai a yammaci Libiya da aikata laifukan yaƙi.

A cikin wani rahoto da ta bayyana ƙungiyar ta zargi ƙungiyoyin mayaƙan daban-daban da aikata kisan gila a kan farar hula makonnin da dama da suka wucce.

Sannan kuma ta ce mayaƙan da ke faɗa tsakaninsu na harba rokoki da makaman atilare a anguwannin da ke cike da jama'a,waɗanda ke faɗawa a kan makarantu da asibitoci da kuma wasu gine-ginen gwamnatin.