An zargi Iran da keta yarjejeniya | Labarai | DW | 22.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi Iran da keta yarjejeniya

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya bayyana cewar Iran ba ta mutunta wani bangare na yarjejeniya da aka yi kan shirinta na nukiliya wanda a ciki aka haramta mata kera makaman kare dangi.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a birnin Brussels na kasar Beljiyam, Minista Le Drian ya ce shi da takwarorinsu na Kungiyar EU za su yi dukannin mai yiwuwa wajen ganin Iran ta mutunta yarjejeniya da aka yi da ita. Baya ga wannan, ministan ya ce za su sake jaddadawa Iran din rashin jin dadinsu game da irin katsalandan da ta ke yi a kasashen Yemen da Lebanon da Siriya wanda a cewarsa na jawo rarrabuwar kai. Ya zuwa yanzu dai Iran ba ta kai ga maida martani kan kalaman na Le Drian ba.