An zargi gwamnatin Sudan da keta hakkin ´yan Adam | Labarai | DW | 28.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi gwamnatin Sudan da keta hakkin ´yan Adam

Hukumar kula da ´yan gudun hijira ta MDD ta zargi gwamnatin Sudan da cin zarafin bil Adam ciki har da azbatarwa, gurbacewar yanayi a gidajen kurkuku da kuma kai hare hare akan fararen hula a lardin Darfur. Bayan an gabatar mata da wani rahoto dake kunshe da hirarraki da masu bincike suka yi da wadanda aka keta hakkinsu da kuma shaidu, hukumar ta yi kira da gwamnatin Sudan da ta kawo karshen wannan al´ada ta muzgunawa a fadin kasar ta Sudan. Tawagar hukumar dai sun je wannan kasa ne don kimanta irin ci-gaba ko akasin haka da aka samu tun kawo karshen wani yakin basasa mafi dadewa a wata kasa ta nahiyar Afirka a cikin watan janerun bara. Yarjejeniyar dakatar da wannan yakin basasan ta ba wa ´yan tawayen kudaancin Sudan damar shiga ciki gwamnati.