An zargi Amirka da kokarin kawar da Putin | Labarai | DW | 08.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi Amirka da kokarin kawar da Putin

Rasha ta ce Amirka na kokarin kawo karshen gwamnatin shugaba Vladmir Putin sabili da irin halin da ake ciki a gabshin Ukraine inda 'yan aware ke tada kayar baya.

Shugaban Rashan Vladmir Putin ya ce Amirka da kawayenta sun dau wannan mataki kan Moscow ne don gallaza mata sakamakon tsayuwar da ta yi kan kafafunta da ma karfin da ta ke karawa.

Mukaddashin ministan harkokin wajen Rashar Sergei Ryabkov ya ce Amirkan na amfani ne da irin takunkumin da ta kakabawa Moscow wajen ganin ta cimma wannan buri nata.

A wani jawabi da ya yi a zauren majalisar dokokin Rashan Mr. Ryabkov ya ce da wuya nan kusa dangantaka tsakanin Moscow da Washington ta daidaita domin kuwa a bayyane ta ke cewar ana yin amfani da takunkumin ne don rusa kasar.