An zargi Adama Barrow da laifin nuna wariya | Zamantakewa | DW | 28.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

An zargi Adama Barrow da laifin nuna wariya

Rundunar sojin Gambiya ta koka da rashin damawa da ita tun bayan da shugaba Adama Barrow ya dare karagar mulki ganin yadda aka mayar da sojin kasar saniyar ware.

Shugaban Gambiya Adama Barrow ya musanta zargin da ake yi wa gwamnatinsa cewar ba ya damawa da rundunar sojin kasar tun bayan da ya dare gadon mulki a farkon wannan shekarar. Shugaban na Gambiya ya ce zance da yanzu haka ya bazu a kasar wanda ke nuni da cewar gwamnatinsa ta mayar da sojin kasar saniyar ware wajen tafiyar da sha'anin mulki labari ne irin na kanzon kurege domin kuwa shi da mukarraban gwamnatinsa sun dauki matakai da dama na ganin sun yi tafiya tare da sojojin kasar, hasalima shiri suka yi na ganin sun sharewa da dama daga cikinsu hawaye saboda irin abinda gwmanatin baya ta yi musu, baya ga batun sojoji da gwamnatin ta Gambiya ta ce ta ja a jiki tare da share musu hawaye, a share guda shugaba Barrow ya ce mutane da dama da suka fice daga kasar a shekarun baya sakamakon rashin jituwa da gwamnatin da ta gabata sun fara dawowa kuma tuni gwamnatinsa ta fara aiki da wasu da nufin ganin an sake gina kasar duba da irin kwarewar da dama daga cikinsu ke da ita.

To baya ga wannan batu shugaban na Gambyiya ya ce kwalliya ta fara biyan kudin sabulu idan aka yi la'akari da irin matakan da suka dauka na ganin lamura sun daidaita a kasar musamman ma dai ta fannin tattalin arziki kazalika kokarin da gwamnatinsa ke yi wajen ganin an samu saukin rayuwa a kasar ya fara haifar da da mai idanu domin kuwa farashin kayan masarufi ya fara sauka.Dangane da rade-radin da ake yi cewar magoya bayan tsohon shugaban kasar ta Gambiya Yahya Jammeh na gudanar da taruka a kasar Mauritaniya da ke makotaka da su don dagula lamura na siyasa a kasar kuwa, Shugaba Barrrow ya ce wannan labari ba shi da sahihanci domin jami'ansu na tsaro sun gundar da bincike kuma ba su ci karo da wani labari makamancin wannan ba.

Sauti da bidiyo akan labarin