1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi ɗan Isra'ila da saidawa Iran makamai

May 12, 2014

Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce jami'an tsaro sun kame wani ɗan ƙasar bisa zarginsa da yin cinikin makamai da Iran.

https://p.dw.com/p/1ByY2
Benjamin Netanjahu
Hoto: picture-alliance/dpa

An kama mutumin ne ɗan shekaru 64 da haihuwa bayan da Amirka ta buƙaci Isra'ilan ta yi haka lokacin da ya ke ƙoƙarin barin ƙasar ta filin jirgin sama.Ma'aikatar shari'ar Isra'ilan ta ce yanzu haka Amirka ta buƙaci a miƙa mata mutumin don a cewarta ta jima ta na nemansa ruwa a jallo saboda zargin saidawa Iran wasu sassa na kayan yaƙi, baya ga laifin da Amirkan ta ce ya aikata a ƙasarta na fidda wasu kayayyaki ba bisa ka'ida ba.

Kafofin watsa labarai a ƙasar ta Isra'ila dai sun ce daga cikin irin abubuwan da mutumin ya saidawa Iran ɗin har da kayayyakin haɗa jirgin yaƙi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahmane Hassane