An zabi sabon shugaban ′yan adawan Siriya | Labarai | DW | 05.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zabi sabon shugaban 'yan adawan Siriya

Sabon shugaban 'yan adawan Siriya Khaled Khoja ya ce ba za su shiga tattaunawa da bangaran hukumomin kasar ta Siriya ba kamar yadda Rasha ta bukaci da yi.

Wannan hadin gwiwa ta 'yan adawar kasar ta Siriya mai cibiya a birnin Istanbul na kasar Turkiya, wanda kasashen yamma suka amince da shi a matsayin 'yan adawar kasar ta Siriya, ya zabi Khaled Khoja a matsayin jagoransa.

Sabon shugaban 'yan adawar ta Siriya ya kara da cewa, ba za su zauna kan teburi guda da hukumomin na Siriya ba, sai fa idan tattaunawa ce za'a girka da hukumomi na rikon kwarya masu cikaken iko.

Kasar Rasha da ake yi wa kallon wadda take dasawa da gwamnatin shugaban Bashar Al-Assad na kasar ta Siriya, ta yi kokarin ganin bangarorin kasar sun koma kan teburin tattaunawa.