An zabi sabon kakakin majalisa a Nijar | Siyasa | DW | 24.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An zabi sabon kakakin majalisa a Nijar

'Yan majalisar dokokin jamhuriyar Nijar sun kada kuri'ar zaben sabon shugaban majalisar dokokin kasar bayan da kotun tsarin mulki ta tabbatar cewa babu kowa bisa kujerar.

A wannan Litinin din ce (24.11.2014) 'yan majalisar dokokin Nijar suka zabi sabon shugaban majalisar dokoki, wanda ya maye gurbin Hama Amadou bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukunci cewa kujerar ta majalisa tamkar babu kowa a samanta ne, tun bayan da Shugabanta Hama Amadou ya yi gudun hijira zuwa kasar Faransa yau kusan watanni uku.

Dan majalisar Amadou Salifou na yankin birnin Yamai shi ne aka dora a wannan mukami, wanda aka zaba a karkashin inuwar jam'iyar MNSD Nassara, madugar adawar kasar, kafin daga bisani ya canza sheka ya zuwa marawa gwamnati baya duk kuwa da rashin amincewar uwar jam'iyar. An dai zabe shi a matsayin sabon kakakin majalisar ta Nijar ne da kuri'u 71 daga cikin 'yan majalisu 76 da suka yi zaben. An dai sha gwagwarmaya kafin ya zuwa wannan zabe tsakanin bengaran masu rinjaye da na 'yan adawa bisa tsarin tafiyar da zaben.

Sai dai kuma kafin a yi wannan zabe, wasu 'yan majalisun na bengaran adawa a kalla 23, sun shigar da wata takardar neman kifar da gwamnatin Briji Rafini, wadda tun watanni da dama suke zargin ta da laifuka masu yawa, wanda zargin ya kai har ga shugaban kasar Issoufou Mahamadou bisa rishin iya tafiyar da harkokin mulki.

Sauti da bidiyo akan labarin