1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Poroshenko ya zama shugaban jam'iyya

Yusuf Bala Nayaya
May 31, 2019

Tsohon shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya karbe ikon jam'iyyarsa a wannan Juma'a, abin da ke zuwa bayan da Poroshenko ke sake samun goyon baya na mambobin jam'iyyarsa watanni gabanin zaben 'yan majalisar Ukraine.

https://p.dw.com/p/3Ja8c
Ukraine Petro Poroschenko
Hoto: Reuters/ Mikhail Palinchak/Ukrainian Presidential Press Service

A watan daya gabata ne dai shugaban da ke samun goyon bayan kasashen yamma ya sha kashi a zaben shugaban kasa inda dan wasan kwaikwayo Volodymyr Zelensky ya kai shi kasa yayin da a kasar ake tsaka da fama da rikicin 'yan aware a gabashi haka batu na cin hanci da rashawa da talauci na gallabar al'ummar kasar ta Ukraine.

Jam'iyyar Poroshenko dai ta sa himma da kokari na jan hankali na magoya baya don ganin ta kai labari a zaben 'yan majalisar da za a yi a ranar 21 ga watan Yuli.  Poroshenko dai shi ke da rinjaye a majalisar mai mambobi 450 sai dai Zelensky na son mamaya a sabuwar tafiya da ya kwaso inda yake bayyana kansa a matsayin bawan al'umma.