Sahle-Work ta zama shugabar kasar Habasha
October 25, 2018Talla
Zaben Sahle-Work na zuwa ne mako guda bayan da firaiminista Abiy Ahmed ya nada mata da dama cikin sabbin ministocin gwamnatinsa.
Sabuwar shugabar mai shekaru 68 ta yi aiki a Majalisar Dinkin Duniya. Sahle-Work za ta maye gurbin tsohon shugaban kasar Mulatu Teshome wanda ya yi murabus daga mukamin.
Sahle-Work ta yi alkawarin aiki tukuru wajen tabbatar da hadin kan al'ummar Habasha a wani yunkuri na kawo zaman lafiya a kasar da ke fama da rikicin kabilanci.