1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace ta yi nasarar darewa kujerar shugabancin majalisar EU

Binta Aliyu Zurmi
January 18, 2022

Roberta Metsola da ke wakiltar kasar Malta a majalisar EU ta yi nasarar darewa kujerar shugabancin majalisar, bayan kwashe shekaru ba a sami mace a wannan matsayin ba.

https://p.dw.com/p/45hhk
Frankreich Straßburg | Wahl der neuen Ratspräsidentin des Europäischen Parlaments Roberta Metsola
Hoto: Jean-Francois Badias/AP Photo/picture alliance

Majalisar dokokin tarayyar Turai ta zabi 'yar majalisar kasar Malta Roberta Metsola a matsayin shugaba a yayin wani zama da majalisar ta yi a yau Talata. 

Nasarar da Metsola mai shekaru 43 ta samu na kuri'u 458 a cikin 616 bayan karawa da wasu takwarorinta mata, ta bata damar zama mace ta farko cikin shekaru da suka gabata da za ta shugabanci majalisar.


Wannan dai na zuwa ne bayan rasuwar tsohon shugaban majalisar David Sassoli. Roberta Metsola ta kasance guda daga cikin mambobin majalisar tun daga shekarar 2013. Dama tana gab da cika wa'adinta na shekaru biyar kafin ta kai ga wannan matsayin.